Sauran kiris Boko Haram ta zamto tarihi - Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, zamanin ta'addanci na kungiyar Boko Haram ya fara shudewa, tare da disashewar adadin sabbin shiga kungiyar a sakamakon tsayin daka na dakarun sojin kasar nan.
Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin karbar bakuncin tare da karamci na jakadan wata babbar coci ta Apostolic Nuncio zuwa ga Najeriya, Rabaran Antonio Guido Filipazzi a fadar sa dake babban birnin kasar nan a ranar talata ta yau.
Buhari ya lura da cewa, kungiyar ta'addancin ta rasa madogara wadda tayi garkuwa tare da tsayuwa akai tun a fari, wanda hakan ke ci gaba da ja bayan ta da kuma kawo ƙarshen ta na dindindin.
KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: 'Yan ƙwallo 13 mafi tarin dukiya
A nasa jawabin, Filipazzi ya bayyana cewa, yana da sha'awar bayar da gudunmuwar sa wajen yakar ta'addanci, cin hanci da rashawa da kuma habakar tattalin arzikin Najeriya.
Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karrama sabbin jakadu na kasashen Nijar da kuma Ghana.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng