Rikicin Beuwe : Dakarun sojojin Najeriya sun fara gudanar da atisayen gudun muzuru a yankin Arewa na tsakiya

Rikicin Beuwe : Dakarun sojojin Najeriya sun fara gudanar da atisayen gudun muzuru a yankin Arewa na tsakiya

- Sojojin Najeriya za su fara gudanar da atisayen gudun muzuru a yankin Arewa na tsakiya

- Shugaban kasa ya gana da hafsoshin jami'an tsaro akan yadda za a kawo karshen rikicn makiyaya da manoma a ranar Litinin

Dakarun sojojin Najeriya za su fara gudanar da atisayen, Gudun muzuru a yankin Arewa na tsakiya a cikin wannan mako dan kawo karshen rikicin manoma da makiyaya a kasar.

Hadimin shugaban kasa a fannin watsa labaru, Mista Femi Adesina ya bayyana haka a wata Bidiyo da ya saka bayan an kammala taron majalissar tsaron kasa da shugaban kasa ,Muhammadu Buhari, ya jagoranta a ranar Litnin.

Adesina ya ce, ”Taron da shugaban kasa yayi da hafsoshin jami’an tsaro a ranar Litinin ya kunshi tattaunawa akan yadda za a kawo karshen rikicin makiayaya da manoma, satar shanu da sauran matsalolin da ya addabi wasu sassan kasar.

Rikicin Beuwe : Dakarun sojojin Najeriya sun fara gudanar da attisayen gudun muzuru a yankin Arewa na tsakiya
Rikicin Beuwe : Dakarun sojojin Najeriya sun fara gudanar da attisayen gudun muzuru a yankin Arewa na tsakiya

“Rundunar sojin Najeriya ta sanar da fara Atisayen Gudun muzuru a yankin Arewa na tsakiya cikin wannan mako.

KU KARANTA : Zaben 2019: Ka koma gida ka hutu, Junaid ya fadawa shugaba Buhari

Ana sa ran wannan mataki zai kawo kasrshen rikicin makiyaya da manoma da ya addabi mutanen yankin.

Wannan ya kara tabbatar wa al’umman Najeriya cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yana kokarin kawo karshen al'amarin sabanin yadda wasu ke gani kamar rikicin bai dame shi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel