Kungiyar mahauta sun koka akan yawaitar sayar da naman jaki a kasuwanin kudu
- Kungiyar mahautan kudu ta zargi Fulani makiyaya da sayar da namun jakuna a yanki kudu
- Mahautan yankin kudu su bakci gwamnati ta dauki mataki wajen hana sayar da namun jakuna a yankin kudu maso kudu
Kungiyar mahautan Najeriya dake yankin kudu maso kudu, sun koka akan yadda ake sayar da namun jakuna a kasuwanin kudancin kasar.
Mahautan sun yi kira ga kungiyar mahautan na kasa, NBUN, da su gaggauta daukan matakin wajen hana wannan mugu aiki.
Mahautan sun yi wannan kira ne a ciki wata sanarwa da suka fitar a ranar Lahadi a birnin Benin bayan sun kammala wani taro da suka gudanar.
Sun koka kwarai akan aukuwan hakan, inda suka yi nu ni da cewa, ba kowa ne ke cin naman Jakunan ba, sannan kuma ba kowa ne zai iya bambancewa a tsakanin naman jakin da na shanu ba.
KU KARANTA : Hukumar NAPTIP ta kama likitan dake siyar da jarirai a Abuja
Rahoton da kungiyar ta fitar ya nu na cewa, da yawa daga cikin masu sayar da naman jakunan a yankin a boye suke yanka jakunan sannan su kwaso naman fili su fara saida wa mutane.
Kungiyar ta ce tana zargin Fulani makiyaya da aikata wannan danyen aikin a sassa daban-daban inda ta nemi gwamnati ta gaggauta daukan mataki akan wannan al’amari.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku ci gaba da bin mu a
Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa
Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng