Wanda ya sake sayen fili a Abuja ya sayi biri a sama - Ministan Abuja
- Ministan Abuja ya bayyana damuwar sa akan harkalar cinikin filaye da gonaki da ake yi a birnin tarayya Abuja
- Mohammed Bello ya ce duk wanda ya sake sayen fili a Abuja ya sayi biri a sama
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Muhammad Bello, ya bayyana damuwa da takaici akan yadda ake harkalar cinikin filaye da gonaki a birnin Abuja.
Mohammed Bello yayi gargadi duk wanda yake da niyyar sayen fili ko gona dake birnin Abuja, ya dakata har sai an kammala sanya sabbin ka’idojin mallakar fili a birnin.
Sakataren hukumar FCT kuma shugaban kwamitin raba filaye, Chinyeaka Ohaa, ya yi wannan jawabi a wani taro da kwamitin ta gudanar a Abuja.
Ya kara da cewa ya zama dole a yiwa mutanen wannan gargadi domin a rage yadda mugayen dilalai filaye ke ci gaba da zambatar masu neman sayen filaye ido rufe a Abuja.
KU KARANTA : Hukumar NAPTIP ta kama likitan dake siyar da jarirai a Abuja
Chinyeaka ya ce duk da an hana sayar da filaye a yankunan Abuja tun a cikin shekara 2006, har yanzu dilalai na ci gaba da sayar wa mutane filaye.
A karshe ya yi kira ga duk wanda ya san gwamnati ta mallaka masa fili , to ya garzayo ya karbi takardar mallakar fili.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku ci gaba da bin mu a
Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa
Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng