PDP ta fara tattaunawa da wasu gwamnonin APC na Arewa ta Tsakiya - Secondus
A ranar Litinin din da ta gabata ne, shugaban jam'iyyar PDP na kasa Cif Uche Secondus ya bayyana cewa, sauran kiris wasu zababbun gwamnoni na jam'iyyar APC a Arewa ta Tsakiya su dirfafi jam'iyyar ta PDP.
Secondus yake cewa, tuni sun fara ganawa da wadannan gwamnoni da a kwana-kwanan za su yi musu tarba ta hannu biyu-biyu a jam'iyyar.
Shugaban jam'iyyar ya bayyana hakan ne a birnin Umuahia na jihar Abia a yayin ziyarar aiki ta yini guda domin ganawa da shugabannin jam'iyyar na jihar.
Legit.ng ta fahimci cewa, jihohi shidda na Arewa ta Tsakiya sun hadar da; Neja, Kogi, Kwara, Benuwe, Nasarawa da Filato wanda duk jam'iyyar APC ce ke jagoranta.
Cif Secondus ya bayyana cewa, gwamnonin jam'iyyar PDP suna nan daram sabanin jita-jitar wasun su zasu sauya sheka zuwa wasu jam'iyyun a sakamakon gabatowar zaben kasa na 2019.
KARANTA KUMA: Jerin ƙasashe 15 mafi arziki a duniya
Ya kuma gargadi hukumar zabe ta kasa wato INEC, akan kada ta kuskura ta yi magudun zabe, inda yake cewa INEC ta sani PDP ba za ta lamunci rashin gaskiya ba.
Ya kara da cewa, gwamnatin jam'iyyar APC ke da alhakin kashe-kashe da kuma rikicin makiyaya a jihar Benuwe da wasu yankuna na kasar nan.
Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne aka tsinto gawar wasu jami'ai biyu na hukumar NSCDC a jihar Benuwe.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng