'Yan sanda sunyi nasarar kwato wasu makiyaya da shanu daga hannun 'yan kungiyar boko haram

'Yan sanda sunyi nasarar kwato wasu makiyaya da shanu daga hannun 'yan kungiyar boko haram

- 'Yan sanda sun kwato makiyaya daga hannun 'yan boko haram

- Kwamishinan 'yan sandan jihar Borno ne ya bayyana hakan ga manema labarai

- An kwato su tare da shanaye 200 a 2 ga watan Fabrairun wannan shekarar

'Yan sanda sunyi nasarar kwato wasu makiyaya da shanu daga hannun 'yan kungiyar boko haram
'Yan sanda sunyi nasarar kwato wasu makiyaya da shanu daga hannun 'yan kungiyar boko haram

Hukumar 'yan sandan jihar Borno ta ceto wasu fulani makiyaya tare da shanu sama da guda 200, daga hannun 'yan boko haram, a karamar hukumar Nganzai.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Mista Damian Chukwu, ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ga manema labarai. Ya ce an kubutar da makiyayan a ranar 2 ga watan Fabrairu, ta hanyar hadin gwiwa tsakanin 'yan sanda da kuma kungiyar (CJTF) a takaice.

Ya bayyana cewar an kai harin ne a lokacin da aka tabbatar da cewar 'yan bindigar sunyi garkuwa da makiyayan sannan suna neman kudin fansa.

'Yan sandan sun samu nasarar ceto makiyayan tare da shanun su, inda 'yan bindigar suka gudu.

DUBA WANNAN: Da alamun hukumar NEDC zata kawo sauyi ga mutanen Arewa maso gabas

Chukwu ya bayyana cewar 'yan sandan sun kaucewa wani hari da wasu mata 'yan kunar bakin wake suka so su kai ofishin 'yan sanda dake Dikwa.

Kwamishinan ya yaba da namijin kokarin da DPO din Nganzai da Dikwa suke yi, na ganin sun kaucewa hare - haren da ake kawo musu.

Yayin da yake jawabi game da 'yan fashi da makami, kwamishinan ya ce an samu nasarar harbe wani dan fashi da makami akan hanyar Askira - Tuga dake karamar hukumar Damboa.

Sannan ya kara da cewar sun samu nasarar kama wani mai suna Peter Ali da motoci guda biyu ba tare da takardun shaida ba, wanda ake zargin ya kara da cewa, an sato motocin daga Abuja ne, shi kuma ya siya a gurin wani Paul James.

"Har ila yau, SARS ta kama Abubakar Umar da mota kamfanin Honda mai lamba AT815 FGE, da aka sato daga Kano. "Sannan an samu nasarar kama wasu mutum uku Taju Muhammad, Abdulrahman Zarami da kuma Babagana Ibrahim da wayoyi selula guda 10, wanda suka sata a wurin kungiyar (NGO).

"Har ila yau 'yan sanda sun samu nasarar kwato wasu injinan lantarki guda 2, 17.5KVA Mikano, wanda aka sato daga kamfanin sadarwa na MTN dake Marte."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel