Sarki Sanusi ya zargi gwamnoin jihar Taraba da Benuwe da daukar nauyin 'yan t'ada wajen tada zaune tsaye a jihohin su

Sarki Sanusi ya zargi gwamnoin jihar Taraba da Benuwe da daukar nauyin 'yan t'ada wajen tada zaune tsaye a jihohin su

- Sanusi Lamido ya ce gwamnonin jihar Taraba da Benuwe suna daukin nauyin yiwa 'yan ta''ada horo da kai wa makiyaya hari a jihohi su

- Sarkin Kano ya bayyana takaicin sa akan daukar hana kiwo a fili da wasu jihohin Arewa suka zartar

Dokar hana kiwo a fili da gwamnatin jihar Taraba da Benuwe ta zartar ya dauki sabon salo yayin da sarkin Kano mai martaba, Muhammadu Sanusi II, ya zargi Gwamnonin da daukar nauyin ‘yan ta’ada dan tada zaune tsaye a jihohin su.

Sanusi yace yana da tabbacin cewa gwamnoni suna dauki nauyin yiwa ‘yan ta’ada horo dan kai wa makiyaya hari a jihohin su, amma duka gwamnonin sun karyata wannan zargi.

A wani taron da yayi da kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) a jihar Niger, Sanusi ya bayyana takaici da damuwar sa akan dokar hana kiwo a fili da gwamnonin suka zartar a jihohin su.

Sarki Sanusi ya zargi gwamnoin jihar Taraba da Benuwe da daukar nauyin 'yan t'ada wajen tada zaune tsaye a jihohin su
Sarki Sanusi ya zargi gwamnoin jihar Taraba da Benuwe da daukar nauyin 'yan t'ada wajen tada zaune tsaye a jihohin su

Yace, “Yana son mataimakin shugaban kasa yayi magana da gwamnonin jihar Taraba, Benuwe, sarakunan gargajiyan Kabilan Tiv da Bachama akan yadda ‘yan ta’ada ke cigaba da zartar da dokar hana kiwo a fili ba a bisa ka’ida ba.

KU KARANTA : Shehu Sani yayi Allah wadai sabon kisan da aka yi a kudancin Kaduna

“Najeriya bata da karfin cigaba a fuskanta rikicin kabilanci, muna sa ran za a zauna a tattauna dan juna dan shawo karshen matsalolin da jihohin ke fuskanta.

Babban hadimin gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, MistaTerver Akase ya karyata zargin da aka yiwa gwamnan jihar.

Akase yace da dagaske gwamnan na daukar nauyin ‘yan ta’ada, da baza su kai wa jihar Benuwe hari ba.

Shima mai magana da yawun bakin gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku, Mista Bala Abu, ya karyata wannan zargi inda yace ba a yiwa gwamnan adalci ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng