Abunda na tattauna da jami'an tsaron Najeriya yayin tattaunawar mu - Shugaba Buhari
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kwarmata wa 'yan Najeriya kadan daga cikin batutuwan da suka tattauna da jami'an tsaron kasar nan yayin tattaunawar sirrin da suka yi a fadar shugaban kasar dake a unguwar Villa, babban birnin tarayyar Najeriya jiya Litinin.
Shugaban kasar ya sanarwa da 'yan Najeriya cewar ya umurci dukkan jami'an tsaron da su kara zage dantse wajen ganin sun kara azama wajen bankado laifuka da masu yunkurin aikata su tun kafin ma su kai ga aikata su.
KU KARANTA: Bakanike ya kashe matar sa saboda da kishi
Legit.ng ta samu cewa shugaban yayi wannan bayanin ne a cikin wani dogayen jerin sakwanni da yayi ta shafin sa na dandalin sada zumunta na Tuwita.
A cewar sa, yanzu dole ne jami'an tsaron farin kaya da da kuma 'yan sanda su kara kaimi da azama wajen gudanar da ayyukan su domin samun dakile dukkan wani rashin tsaron dake addabar kasar.
A wani labarin kuma, Shugaban jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, watau Prince Uche Secondus ya bayyana cewa a halin yanzu 'yan kasar nan na fuskantar wani irin bakin mulki mai cike da son kai da rashin adalci a karkashin shugabancin shugaba Muhammadu Buhari da kuma jam'iyyar All Progressives Congress karara.
Mista Uche Secondus ya yi wannan ikirarin ne a yayin da yake zantawa da wasu 'yan majalisun tarayyar Najeriyar a karkashin inuwar jam'iyyar su a ranar Talatar da ta gabata ne a garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng