Karin matsayi: Hotunan wani Bahaushe da ya bude wurin saida suya a birnin Landan
Allah ya tarfa sana'ar wani bahaushe dan asalin Najeriya mai suna Abdullahi MaiKano nono yayin da ya bude shagon sayar da suya a birnin Landan, lamarin da yayi matukar kayatar da 'yan Najeriya mazauna can Landan din da kuma gida Najeriya.
Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, matashin an ce yana da shaidar karatun boko mai daraja ta digiri na biyu wanda kuma ya kammala karatun sa a jami'ar Greenwich dake a birnin na Landan.
Legit.ng ta samu cewa sai dai abunda ya kara kayata lamarin shine yadda 'yan Najeriya a duk inda suke suke da kishin gida Najeriya da kuma kokarin habaka al'adun su da kuma neman na kansu.
A wani labarin kuma, mun kawo maku labarin wasu masu sana'ar kamun kifi a wani bangare na duniyar nan sun ga abun al'ajabi bayan da suka kamo wani irin kifi mai dogon bakin da ke kama da zarto da ba kasafai aka cika ganin sa ba.
Mun samu dai cewa hotunan kifin da suka bazu a kafar sadarwar zamani sun dauki hankulan jama'a inda kowa yake tofa abarkacin bakin sa game da su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng