Wani mutum bakanike ya buge matar sa har lahira saboda kyawun ta
Wani labari maras dadin ji da muka samu daga majiyar mu ta Punch na nuni da cewa wani bakanike mai gyaran tayar mota a garin Mbiabam Ibiono na karamar hukumar Ibiono Ibom a jihar Akwa Ibom mai suna Nkere Uta ta make matar sa mai suna Bella Uta har lahira a jiya Litinin.
Kamar dai yadda muka samu, ma'auratan da suka shafe shekaru da yawa a tare suna da 'ya'ya biyar kafin aukuwar lamarin da yayi matukar girgiza al'ummar yankin.
KU KARANTA: Shehu Sani yayi Allah-wadai da sabon harin da aka kai jihar Kaduna
Legit.ng dai ta samu cewa ana zargin mijin ta ne da aikata wannan mummunar ta'asar saboda tsananin kishin da ke gareshi da kyawon da Allah ya yi mata shi kuma bai da kudi sosai.
Haka nan kuma majiyar ta mu ta samu cewa a baya an zargi mijin da matsalar tabin hankari amma sai aka ce ya warke.
Yanzu haka dai yana hannnun jami'an 'yan sanda.
A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya dake a garin Legas a ofishin 'yan sandan garin Itire sun sanar da samun nasarar cafke wani matashi mai suna Samson Aghedo bisa zargin sa da suke yi da lakadawa abokiyar aikin su bugun tsiya.
Labaran da muka samu dai sun bayyana cewa 'yar sandan dai ta je ta kamo mutumin ne a gidan sa dake a kan titin Ola mai lamba 32 saboda wani laifin da ya aikata amma sai ya hauta da bugu daga bisani.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng