Karancin mai: Manyan jirage 36 makare da mai sun iso tashar jirgin ruwan Legas

Karancin mai: Manyan jirage 36 makare da mai sun iso tashar jirgin ruwan Legas

Akalla jirage 36 ne makare da man fetur da dangogin su tare da kuma abincin masarufi ake dakun isowar su tashar jiragen ruwan Apapa da Tin Can dake a gabar ruwan Najeriya, hijar Legas daga 12 ga watan Fabreru zuwa 24 ga watan kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu.

Hukumar gwamnatin tarayya dake kula da harkokin tashoshin ruwan kasar watau Nigerian Ports Authority (NPA) a turance ce ta sanar da hakan a cikin wani sako da take fitarwa a kai a kai da kuma kamfanin dillacin labarai ya samu.

Karancin mai: Manyan jirage 36 makare da mai sun iso tashar jirgin ruwan Legas
Karancin mai: Manyan jirage 36 makare da mai sun iso tashar jirgin ruwan Legas

KU KARANTA: An yankewa wanda ya sace yan matan Chibok hukunci

Legit.ng ta samu haka zalika cewa sauran abubuwan da jiragen ruwan za su zo da su sun hada da takin zamani, suga, kifi da dai wasu kayan ma'adanai da kuma na masarufi.

A wani labarin kuma, Jami'an hukumar dake hana fasa kwaurin kayayyaki ta tarayyar Najeriya sun sanar da samun nasarar cafke wata hodar ibilis mai yawan gaske a cikin wasu kayan daki da akayi kokarin shigowa da su cikin kasar nan.

Jami'an dai sun bayyana cewa hodar ibilis din dai da suka kama ta kai yawan ma'aunin kilogiram 317.5 sannan kuma an saka tane a cikin gadaje da kuma kayan kicin din da aka dauko daga kasar Puerto Rico.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng