Nigerian news All categories All tags
Hukumar NAPTIP ta kama likitan dake siyar da jarirai a Abuja

Hukumar NAPTIP ta kama likitan dake siyar da jarirai a Abuja

- Hukumar NAPTIP ta kama likitan dake siyar da jarirai a Abuja

- Likitan dake siyar da jarirai a Abuja yana shiryawa da matan da basu da haihuwa kafin ya sayar musu da jarirai

Hukumar yaki da masu fataucin dan Adam NAPTIP ta tona asirin wani likita da ta kama ya na siyar da jarirai a asibitin sa dake unguwar Nyanya a birnin Abuja.

Mai magana da yawun hukumar NAPTIP, Josiah Emerole, da ya sanar da haka ya ce sun kama shugaban asibitin ‘Akuchi Herbal Concept’ da laifin siyar da jarirai ga matan da basu iya haihuwa.

Hukumar NAPTIP ta kama likitan dake siyar da jarirai a Abuja

Hukumar NAPTIP ta kama likitan dake siyar da jarirai a Abuja

Emerole ya kara da cewa likitan yakan shirya da mata da basu da haihuwa su yi ciniki sannan sau bashi kudi masu yawa.

KU KARANTA : Najeriya zata fitar da gangan danyen man fetur miliyan daya a watan Janairu na shekara 2019 - TOTAL

"Matan suna yaudarar mutanen gari da nuna musu kamar suna dauke da juna biyu amma karya ne.

"Bayan watanni tara sai su dawo asibitin su biya shi sannan ya basu sabin jariran da matan da ya aje suka haifa," Inji Emorele

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel