Sharrin shaidan ne, cewar wani Fasto da aka kama da laifin satar Motocin alfarma
Babban limamin cocin ‘God’s Favour Ministry’, Daniel Onwugbufor ya shiga hannun jami’an rundunar Yansandan jihar Ogun a sanadiyyar kama shi da laifin satar motocin jama’a, inji rahoton Premium Times.
Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya bayyana cewa sun kama Faston ne tare da abokin satarsa, Israel Animashaun a ranar 1 ga watan Feburairu a karkashin jagorancin jarumin dansanda Uba Adam na rundunar SARS.
KU KARANTA: Baran ɓarama: Wani direban bankaura ya aika da mutane har guda 7 zuwa barzahu
“Mun samu nasarar cafke barayin ne bayan da muka gano wata mota kirar Lexus RX 330 SUV, da aka sace, a gidan Faston dake unguwar Iba, inda nan da nan muka yi caraf da shi, daga nan kuma ya tona abokinsa Animashaun.” Inji Kaakakin.
A nasa jawabin, majiyar Legit.ng ta ruwaito Animashaun yana fadin a duk lokacin da suka saci mota, Faston su ke kaima wa, don ya siyar musu da ita, amma Faston na cutarsa, inda yace bayan sun saci motar Lexus, N350,000 kacal Faston ya bashi.
Animashaun yace ya taba yin fashin wata babbar waya, kirar Galaxy Samsung, wanda yace Faston ya siya a kan kudi N35,000. Sai dai kash! Faston ya musanta taba sanin Animashaun a matsayin dan fashi da makami, sa’annan kuma ya danganta alakarsa da shi a matsayin sharrin shaidan.
Daga karshe Faston ya yi alkawarin basu rundunar Yansandan jihar hadin kai don ganin an kamo wani abokin satarsu dake garin Onitsha, wanda shi ma yake bashi motocin sata don ya siyar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng