Biki wan shagali: Shugabannin kasashe 5 za su halarci bikin diyar Dangote, Fatima

Biki wan shagali: Shugabannin kasashe 5 za su halarci bikin diyar Dangote, Fatima

- Wanda yafi kowa kudi a duniya, Bill Gate ya sanar da zuwan sa daurin auren diyar Dangote

- Diyar ta Dangote, Fatima zata auri dan tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya M. D. Abubakar

- Haka ma shugabannin kasashe 5 za su halarci bikin

Kawo yanzu dai mun samu daga majiyoyin mu cewa akalla shugabannin kasashe biyar ne suka tabbatar da sha'awar su ta zuwa bikin diyar shahararren mai kudin nan na Nahiyar Afrika watau Fatima Aliko Dangote.

Biki wan shagali: Shugabannin kasashe 5 za su halarci bikin diyar Dangote, Fatima
Biki wan shagali: Shugabannin kasashe 5 za su halarci bikin diyar Dangote, Fatima

KU KARANTA: Adam A. Zango ya sha ruwar duwatsu a garin Gombe

Haka nan ma dai mun samu cewa shi ma dai mai kudin nan na duniya kuma mai kamfanin kera kwamfutocin nan watau Bill Gate shima ya sanar da zuwan na sa.

Legit.ng ta samu dai cewa an bayyana watan maris mai kamawa a matsayin watan da za'ayi bukin da ake sa ran zai zama uba ga dukkan wani bikin da aka tabayi a Najeriya.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa rundunar sojin kasar Ghana dake a yammacin Afrika na sanar da yankewa gawar wani sojan ta da ya mutu a wani hadari tare da abokin sa mawakin da ya raka zuwa wurin wani wasan rawa hukuncin kwanaki 40 a dakin horo.

Kamar dai yadda muka samu, rundunar ta bayyana wannan hukuncin ne ga gawar sakamakon abun da ta kira karya da sojan yayi wa rundunar kafin mutuwar sa inda ya rubuta yana son a bashi hutu don bai da lafiya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng