Yanzu-Yanzu: An gano 2 daga cikin 'yan sanda 4 da suka bace a jihar Benue

Yanzu-Yanzu: An gano 2 daga cikin 'yan sanda 4 da suka bace a jihar Benue

- An gano 2 daga cikin 'yan sanda 4 da suka bace a jihar Benue

- Wannan dai na kunshe a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar mai suna ASP Moses Joel ya fitar

- Sun dai bace a satin da ya gabata a wani kauye da ake kira Azage dake a karamar hukumar Logo

Labarin da muke samu da dumi-dumin sa na nuni ne da cewa rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Benue ta sanar da gano biyu daga cikin jami'an ta hudu da suka bace a satin da ya gabata a wani kauye da ake kira Azage dake a karamar hukumar Logo a raye.

Yanzu-Yanzu: An gano 2 daga cikin 'yan sanda 4 da suka bace a jihar Benue
Yanzu-Yanzu: An gano 2 daga cikin 'yan sanda 4 da suka bace a jihar Benue

KU KARANTA: Za'a fara ansar Naira a kasat Ingila

Wannan dai na kunshe a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar mai suna ASP Moses Joel ya fitar ya kuma rabawa manema labarai a jiya da dare.

Legit.ng dai ta samu cewa a kwanan baya, jami'an 'yan sandan sun sanar da bacewar jami'an na ta hudu inda kuma ta tabbatar da cewa tuni ta tura wasu jami'an nata na musamman domin gano su.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari a ta hannun babban Ministan Shari'a na kasar Malam Abubakar Malami a yau Litinin ne za ta cigaba da yi wa 'yan Boko Haram din da ake zargi da kashe-kashe shari'a.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar damai magana da yawun Ministan Mista Salihu Isah ya fitar ya kuma rabawa manema labarai a jiya Lahadi inda ya bayyana cewa za'a cigaba da shari'ar ne a wani kebantaccen wuri a garin Kaiji dake a jihar Neja.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng