Jirgin Rasha ya yi hatsari da fasinjoji 71 a Moscow

Jirgin Rasha ya yi hatsari da fasinjoji 71 a Moscow

- Shugaban kasar Rasha ya ba da umarnin gudanar da binciken abun da ya janyo hatsarin jirgin sama a Moscow

- Rahotanni sun nuna duka mutanen dake cikin jirgin da yayi hatsari a garin Moscow sun mutu

Wani jirgin sama dake dauke da fasinjoji 71 ya fadi jim kadan bayan ya tashi a filin jirgin sama na Domodedovo dake birnin Moscow a kasar Rasha a ranar Lahadi.

Jirgin saman na kamfanin Saratov ya bace ne bayan tashi sama inda ya fado kusa da kauyen Argunovo dake arewa maso gabashin birnin Moscow.

Jirgin sama na kamfanin Saratov ya fado ne kusa da kauyen Argunovo bayan ya samu matsala a lokacin da ya tashi sama da kilomita 80 daga arewa maso gabashin birnin Moscow.

Jirgin Rasha ya yi hatsari da fasinjoji 71 a Moscow
Jirgin Rasha ya yi hatsari da fasinjoji 71 a Moscow

Jami'ai sun shaidawa kafofin watsa labarai na Rasha cewa ana kyautata zaton daukacin fasinjoji 65 da ma'aikatan jirgin 6 sun mutu.

KU KARANTA : Boko Haram: Najeriya za ta ci gaba da yi wa wadanda ta kama shari'a

Jirgin yayi hatsari ne a lokacin da yake kan hanyarsa zuwa jihar Orsk kusa da kan iyakar Rasha da kasar Kazakhstan kuma ya fado ne da tsakar rana.

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya mika ta'aziyarsa ga iyalan wadanda ke cikin jirgin kuma ya umurci jami'an tsaron kasar su gudanar da bincike dan gano abun da ya janyo hatsarin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng