Yarinya mai shekaru 11 da yayanta mai shekaru 14 ya yiwa ciki ta haihu
- Wata yarinya mai shekaru 11 ta haife cikin da yayanta mai shekaru 14 ya yi mata, kamar yadda jaridar Mirror ta nahiyar Turai ta rawaito
- 'Yan sanda na gudanar da bincike a kan dan uwan yarinyar, da suke uba daya, wanda ya yi mata cikin tun yana da shekaru 13
- Rahotanni sun bayyana cewar hatta iyayen yarinyar basu san tana dauke da juna biyu ba saida suka kai ta asibiti domin duba ciwon ciki dake damunta
Wata yarinya mai shekaru 11 kacal a duniya ta haife cikin da dan uwanta da suke uba daya ya yi mata, kamar yadda jaridar Mirror ta nahiyar Turai ta rawaito.
Yarinyar ta haihu ne a asibitin Virgen de la Arrixaca dake garin Murcia a kudu maso gabashin kasar Sifen.
Yanzu haka 'yan sanda na gudanar da bincike a kan dan uwan yarinyar da yayi mata cikin tun yana da shekaru 13 a duniya.
Rahotanni sun bayyana cewar iyayen yarinyar 'yan asalin garin Bolivia, basu san yarinyar na dauke da juna biyu ba saida suka kai ta asibiti domin duba lafiyar ta bayan yawaitar yi masu korafin fama da matsanancin ciwon ciki.
DUBA WANNAN: An damke gardawa 8 da suka yiwa yar shekara 13 fyade har tayi ciki
Hukumar asibitin ne suka sanar da jami'an 'yan sanda jim kadan bayan yarinyar ta haihu.
Yarinyar da jaririnta na cikin koshin lafiya kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
A shekarar 2013 ne kasar Sifen ta yi gyara a kan dokar shekarun da ya kamata mace ta iya saduwa da namiji, inda ta ayyana shekaru 16 a matsayin mafi karancin shekarun fara saduwa matukar ba fyade aka yiwa yarinyar ba kuma wanda ya sadu da ita babu fifikon shekaru masu yawa tsakaninsu.
Saboda karancin shekarun yaron ba lallai hukumomi su dauki matakin shari'a a kansa ba.
Ministan lafiya a kasar Sifen, Manuel Villegas, ya ce za a gudanar da gwajin kwayoyin halitta na DNA domin tabbatar da ko yaron ne uban jaririn da yarinyar ta haifa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng