2019: Sunayen ministocin Buhari zasu yi murabus domin takarar Gwamna a jihohinsu
- Gabanin zaben 2019, ana sa raai wasu ministoci zasu yi murabus domin takarar gwamna a jihohinsu
- Watakil zasu fafata da gwamnonin jam'iyyarsu ne a cikin gida
- A yanzu dai APC ke mulkin mafi yawan jihohi, musamman a arewa
A yayin da ake saura watanni shida a shiga zabukan cikin gida na jam'iyyu, ana sa rai sghugaba Buhari zai sanya wasu ministocinsa su yi murabus, domin su fuskanci burinsu na siyasa, na zama gwamnoni a jihohinsu.
A lissafin INEC dai, a jaddawalinta, jam'iyyu a bana zasu fitar da masu takara su mika sunayensu tsakanin watannin Agusta zuwa watan Octoba. Wannan dai na nufin abun yazo, inji mai jiran haihuwa.
DUBA WANNAN: Yara kanana ne suka yi zaben kananan hukumomi
Ministoci masu jiran tsammani a jiohinsu dai, sun hada da Aisha Alhassan ministar mata, da Adebayo Shittu na Sadarwa, Mansur da Ali, ministan tsaro, karamin Ministan Makamashi da ayyuka, Suleiman Hassan. Sai karamin Ministan mai Ibe Kachikwu.
Sai kuma Ministan Albarkatu, Kayode Fayemi, mai kokarin kayar da gwamnansa na Ekiti, wanda ya kayar da shi a zaben 2014, lokacin yana neman tazarce, zargi da ake yi cewa tsohon shugaba Jonathan ne yayi masa murdiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng