Jerin ƙasashe 15 mafi arziki a duniya
Cikin kusan ƙasashe 200 a fadin duniya, da yawan su kan samu maƙudan kudade da har a wani sa'ilin suke zarce biliyoyan kudi wajen kudaden shiga da kowace ƙasa take samu a duk shekara.
Wannan ƙididdiga ta samo tushe ne daga cibiyar kudi ta duniya (Internation Monetary Fund, IMF), da ta fitar tun a watan Oktoba na shekarar 2017 da ta gabata, dangane da yadda kowace ƙasa ke karkatar da akala ta tattalin arziki.
Legit.ng ta fahimci cewa, wannan ƙasashe sukan samu yalwar arziki ta fuskar dangartakar harkokin kasuwanci da kuma alaƙar darajoji na kudin ƙasar kamar yadda cibiyar ta IMF ta bayyanar.
Mafi akasarin wannan ƙasashe da suke a sahu na farko akwai irin su ƙasar Brunei da Qatar, wadanda suke samu ƙarfin tattalin arziki wajen hada-hadar man fetur da ma'adanan sa. Harkokin sanya hannun jari da ta'ammali da bankuna su ke habaka tattalin arziki a irin ƙasashen Iceland da kuma Ireland.
Ga jerin ƙasashe 15 dake da ƙarfin gaske a duniya ta fuskar arziki:
15. Iceland
14. Netherlands (Holland)
13. Saudi Arabia (Saudiya)
12. United States (Amurka)
11. San Marino
10. Hong Kong
KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya rasa 'yan uwa biyu a cikin gajeren lokaci
9. Switzerland
8. United Arab Emirates (Daular Larabawa)
7. Kuwait
6. Norway
5. Ireland
4. Brunei
3. Singapore
2. Luxembourg
1. Qatar
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito, akwai jiga-jigai shidda na jam'iyyar PDP dake hankoron samun tikitin takara na jam'iyyar a zaben 2019.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng