Sojojin bogi sun yiwa sojan gaske fashi, sun shiga hannu
- Wasu sojojin bogi guda biyu da suka yiwa wani saja a hukumar soji sun fada komar 'yan sanda
- Sun yiwa sojan fashi ne a hanyar sa ta tafiya jihar Neja daga Abuja
- Sojojin bogi na yawan yin fashi ga matafiya a kan hanya Abuja zuwa Kaduna
Wasu sojojin bogi guda biyu da suka yiwa wani mai mukamin saja a hukumar sojin Najeriya, Usaman Saidu, fashi sun shiga hannun jami'an 'yan sanda.
Sun yiwa Saja saja Saidu, mazaunin barikin sojin Asokoro, fashin ne a daidai dutsen Zuma dake daf da birnin Abuja a yayin da yake dawowa daga jihar Naija.
Jami'an hukumar 'yan sandan jihar Naija sun tabbatar da cewar wadanda aka kama din, Peter Ali da Paul Isyaku, sun dade suna yiwa matafiya fashi ta hanyar yin basaja a matsayin sojoji.
DUBA WANNAN: Yadda wani jirgin yakin sojin Najeriya ya yi luguden wuta a maboyar 'yan Boko Haram tare da lalata wata motar su ta yaki (Bidiyo)
Jami'an 'yan sanda sun bi sahun barayin ne bayan sun yiwa saja Saidu fashin motar sa kirar Honda Accord.
Daya daga cikin wadanda aka kama, Ali, ya ce sun kai a kalla shekaru biyar suna aikata fashi a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna kuma su shida ne.
A labaran Legit.ng kun sha karanta labaran masu aikata miyagun laifuka ta hanyar yin amfani da kakin soji.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng