Shugaba Buhari ya rasa 'yan uwa biyu a cikin gajeren lokaci

Shugaba Buhari ya rasa 'yan uwa biyu a cikin gajeren lokaci

A ranar Asabar ta yau, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi rashin 'yan uwan sa biyu cikin gajeren lokaci.

Hadimi na musamman ga shugaban kasa Mallam Garba Shehu, shine ya bayar da wannan sanarwa a wata ganawa da 'yan jarida.

Kakakin fadar shugaban kasar ya bayyana cewa, shugaba Buhari ya yi rashin 'yan uwan sa biyu daga cikin dangin sa na nesa cikin 'yan sa'o'i kadan.

Mallam Garba yake cewa, an binne Hajiya Halima Dauda ne a safiyar yau asabar a garin Daura, wadda 'yar uwa ce ga shugaba Buhari kuma ta kasance kanwa ga jinin sa, Mamman Daura.

Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

Ta rasu tana da kimanin shekaru 56 a duniya, inda ta bar 'ya'ya 10, mata shidda da maza hudu da suka hadar har da hadimin na musamman ga shugaban kasar, Muhammad Sabi'u Tunde.

Mallam Garba ya ci gaba da cewa, shugaban ma'aikata na fadar shugaban kasa, Abba Kyari, shine ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya har makarbatar da aka sanya marigayiya Halima a makwanci.

Legit.ng ta fahimci cewa, sauran'yan tawagar sun hadar da karamin ministan sufurin jiragen sama; Hadi Sirika, hamshakan 'yan kasuwa biyu; Alhaji Isma'ila Isa da Sayyu Dantata, hadimai uku na musamman ga shugaba Buhari; Sarki Abba, ya'u Darazo, da kuma Shehu.

KARANTA KUMA: Wani ɓarawo mai sabon salon sata ya shiga hannu a jihar Gombe

Sauran 'yan tawagar sun hadar da; sabon shugaban hukumar NIA; Ahmed Rufa'i Abubakar, sakatare na dindindin a fadar shugaban kasa; Jalal Arabi da kuma shugaban hidima na fadar; Ambasada Lawal Kazaure.

Kakakin fadar ya kara da cewa, a ranar Juma'ar da ta gabata ne, dangin shugaban kasar suka binne Hajiya Aisha Alhaji Mamman, wadda ita ce uwargida ga babban yaya na shugaban kasa, Alhaji Mamman.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: