Allah buwayi: Hotunan wani kifi mai ban al'ajabi da wasu masunta suka kama
- Hotunan wani kifi mai ban al'ajabi sun bayyana a kafafen sadarwar zamani
- Kifin dai an bayyana cewa ba kasafai ake samun sa ba
- Kifin yana da wani irin dogon baki ne mai kama da zarto
Wasu masu sana'ar kamun kifi a wani bangare na duniyar nan sun ga abun al'ajabi bayan da suka kamo wani irin kifi mai dogon bakin da ke kama da zarto da ba kasafai aka cika ganin sa ba.
KU KARANTA: Barawo mai sabon salon sata ya bulla a Gombe
Legit.ng ta samu dai cewa hotunan kifin da suka bazu a kafar sadarwar zamani sun dauki hankulan jama'a inda kowa yake tofa abarkacin bakin sa game da su.
Kifin dai yana da girma sosai sannan kuma yana da dogon baki dake dauke da hakora jere a bakin daga gefen sa kamar dai yadda zarton yankan katako yake.
Lallai Allah ya cika abun godiya kuma abun bauta.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng