Wani ɓarawo mai sabon salon sata ya shiga hannu a jihar Gombe
Wani mutum ya shiga hannun hukuma a jihar Gombe, bisa aikata laifin satar babur da yayi kokarin arcewa da shi kafin a ciyo kugun sa.
Wannan barawo dai ya shiga hannu ne a yayin da ma'aikatan tsaro na babban asibitin jihar Gombe suka hangi alamun rashin a tattare da shi wanda hausawa ke cewa ko a cikin ruwa sai anyi jibi.
Ma'aikatan tsaron sun cafke shi ne yana ta kici-kice wajen ballen kan babur domin samu damar yin awon gaba dshi salin alin, sai dai da yake dubu ta cika akan sa ya shiga hannu.
KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun salwantar da rayuka 3 a harin jihar Benuwe
Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin binciken wannan barawo, an same shi tattare da katin shaidar ma'aikatan 'yan sanda har kashi uku daban-daban, wanda wannan lamarin ya kara tabbatar da cewa ya shahara da aikata ta'addanci na halin bera.
A yayin haka kuma, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wasu 'yan bindiga sun salwantar da rayuka uku a wani sabon hari da suka kai kauyen Tsokwa a jihar Benuwe.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng