Kada jawabin Shekau ya yaudareku, suna shirin kai sabbin hare-hare ne - Ahmed Salkida
Ahmad Salkida, wani dan jaridan da ya shahara da alaka da Boko Haram yace kada a yaudaru da sanyin da Shekau yayi a sabon faifan bidiyo da ya saki wanda ke nuna gayiyansa.
Shekau ya saki sabuwar bidiyo inda yace ya gaji kuma ya gwammace ya mutu kawai ya shiga Aljannaha ya huta.
Yace: “Suna na Abubakar Shekau, babban gagararren makiyin da kuke yaka. Wannan shine matsayarmu. Na gaji da wannan rikici, gwanda in mutu inje Aljannah in huta.”
Ahmed Salkida yace: “Idan muka duba jawabin da Shekau yayi a sabon bidiyo cewa ya gaji kuma ya gwammace ya mutu a matsayin mun kayar da shi, to lallai mun jahilci akidarsu na ‘akashe ko a mutu’."
“Shekau ya horarda maza da mata dubunni da bai ma san iyakansu ba, kana wasu na ganinshi a matsayin wani cikas ne wajen cimma burinsu. Ko shakka babu shine shugabansu amma ba shi ke gudanar da abubuwa ba."
KU KARANTA: Kasar Saudiyya ta zanatarwa wani dan Najeriya haddin shigo da muggan kwayoyi
Jaridar Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa shugaban kungiyar Boko Haram ya saki sabon faifan bidiyo inda ya nuna gajiyarsa da wannan yaki jim kadan bayan hukumar soji ta alanta cewa ai ta karashe ragowan Boko Haram.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng