Gwamna Ganduje ya taimaka wa masu sana'ar A Daidaita Sahu a jihar Kano
- Gwamna Ganduje ya tallafawa samari 2,500 da kayan aiki na sana'a
- An koyar da samarin gyaran babur, an basu baburan, da kayan gyara, an kuma koya musu taiyar da sana'ar
- Ana so a rage masu zaman jagaliya a Kano
A bikin yaye dalibai da gwamna Ganduje yayi, na samari akalla 2,500, wadanda ake koya musu sana'ar keke da taxi, sun samu horo da atisaye mai kyau.
An koya musu keke napep, gyaransa da kuma tafiyar da shi, da ma mu'amala da Fasinja
Wannan dai na nufin akalla mutum 100,000 ne zasu mori wannan tagomashi daga gwamnati, ganin cewa kowannensu zai taimakawa iyalinsa, da iyayensa, da ma wasu dangi.
DUBA WANNAN: Da kyar aka kwaci shugaban APC daga hannun wasu fusatattun matasa
A jihar ta Kano, akwai 'yan jagaliya bilaa-adadin, kuma ana zargin gwamnatoci da koya musu shashanci ba sana'a ba, saidai wannan karon, gwamnatin na kokarin magance matsalar ta zaman banza da kashe wando, da ma ci da zuci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng