Jiga-jigai 6 dake hanƙoron tikitin takara na jam'iyyar PDP
Jam'iyyar adawa ta PDP ta yanke shawarar cewa, har yanzu ƙofa bude take ga duk jiga-jigan ta masu sha'awarar tikitin ta na takarar shugaban ƙasa a zaben 2019, inda masu ruwa da tsaki suka zura idanu domin ganin wanda zai yunƙuro a farko.
A yayin da majalisar dokoki ta ƙasa ta sauya tsarin gudanar da zaben 2019, da hakan bai taba faruwa ba a tarihin kasar na gudanar zaben shugaban ƙasa a ƙarshe, ya sanya siyasar ƙasar ta dauki wani sabon salo.
A sakamakon haka ne, guguwar siyasa ta fara rurruma inda 'yan siyasa ke ci gaba da ƙwanƙwashe da jam'iyyu suka fara hanƙoron wadanda zasu kafa a kujerun gwamnati.
Da sanadin jaridar Daily Trust, Legit.ng ta kawo muku jerin jiga-jigan jam'iyyar PDP dake hankoron tikitin tsayawa takara a zaben 2019:
1. Ahmed Makarfi
Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa baki daya.
2. Atiku Abubakar
Tsohon shugaban kasa da ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP
3. Sule Lamido
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, wanda ya kasance tsohon dan majalisar wakilai kuma tsohon ministan harkokin kasashen ketare a lokacin gwamnati Obasanjo.
4. Mallam Ibrahim Shekarau
Shekarau ya kasance tsohonn gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan ilimi na gwamnatin Goodluck.
5. Ibrahim Hassan Dankwambo
Gwamnan mai ci na jihar Gombe, da ya fara hankoro kujerar shugaban kasa tun a da jam'iyyar ta sha kashi a zaben 2015.
KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya bayar da lamunin sallamar manyan alƙalai biyu daga aiki
6. Sanata David Mark
Tsohon shugaban majalisar Dattawa, da ya kasance tsohon gwamnan jihar Neja a lokacin mulkin soja.
A yayin haka kuma, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, 'yan fashi sun kai hari filin jirgin sama na jihar Legas a ranar Juma'ar da ta gabata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng