Buhari yayi ta’aziya ga Buratai kan rasuwar mahaifinsa
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ta’aziya ga babban hafsan sojin kasar, Laftanal Janar Tukur Buratai kan rasuwar mahaifinsa
- A sakon gaisuwar shugaban kasar yace kasar Najeriya bazata taba mantawada kokarin Alhaji Yusuf Buratai gareta ba
- Mahaifin shugaban hafsan sojin ya rasu a safiyar ranar Juma’a, 9 ga watan Fabrairu a Maiduguri
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ta’aziyya ga iyalan Buratai kan rasuwar Alhaji Yusuf Buratai, mahaifinsa babban hafsan soji, laftanal Janar Tukur Buratai.
Sakon ta’aziyyar Buhari na kunshe ne a wata sanarwa daga hannun Mista Femi Adesina, mai ba shugaban kasa shawara na musamman a k,afofin watsa labarai a Abuja a ranar Juma’a.
Sanarwan yace Buhari ya taya iyalan gwarzo a yakin duniya na biyu jimamin mutuwarsa.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya aika sakon fatan alkhairi ga tawagar Najriya a gasar Olympics na 2018
A cewar shugaban kasar Najeriya bazata taba mantawada kokarin Alhaji Yusuf Buratai gareta ba.
Yayi addu’an Allah ya gafartawa marigayin.
A baya Legit.ng ta kawo cewa Mahaifin shugaban hafsan sojin ya rasu a safiyar ranar Juma’a, 9 ga watan Fabrairu a Maiduguri.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng