Wahalar Mai: 'Yan Najeriya na shan bakar ukuba yayin da litar mai ta kai Naira 400
- Yan Najeriya na shan bakar ukuba yayin da litar mai ta kai Naira 400
- Kimanin shekara daya kenan dai da layukan mai suka yi kaura
- Matafiya ma suna ta kokawa inda suka bayyana cewa kudin mota ya karu matuka
'Yan Najeriya da dama na cikin shanukuba bayan da da yawa suka zabi zaman cikin gida sakamakon bala'in tsada da man fetur yayi wanda kuma hakan yayi sanadiyyar tashin farashin tafiye-tafiye inda ake sayen litar mai a kan Naira 400 a wasu wuraren.
KU KARANTA: Da kyau shugaban APC ya sha a hannun samari
Kimanin shekara daya kenan dai da layukan mai suka yi kaura daga Najeriya amma sai gashi sun dawo a watan Disemba kuma kawowa yanzu inda kuma lamarin ya kara ta'azzara kawo yanzu.
Legit.ng ta samu daga kafar sadarwar zamani ta tuwita, Gwamnan jihar Benue dake a yankin Arewa ta tsakiya watau Gwamna Samuel Ortom ya bayyana cewa yana nan yana nazarin barin jam'iyyar sa ta APC ya zuwa jam'iyyar PDP.
Wannan dai na kunshe ne a wani sakon rubutu da Sanatan nan dake wakiltar mazabar yankin Jihar Bayelsa, Sanata Ben Murray-Bruce ya wallafa a shafin sa na Tuwita inda ya bayyana cewa Gwamnan na jihar Benue ya tabbatar masa da hakan.
Haka ma dai matafiya ma suna ta kokawa inda suka bayyana cewa kudin mota ya karu matuka sakamakon hakan.
A wani labarin kuma, A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Ribas dake a kudu-maso-kudancin Najeriya Mista Nyeson Wike ya bayyana cewa tabbas jam'iyyar adawa ta PDP ce zata fatattaki shugaba Buhari zuwa garin sa Daura a zaben 2019 da za'a gudanar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala taron kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta PDP da ya samu halartar jiga-jigan jam'iyyar a garin Asaba, jihar Delta da yake zantawa da manema labarai.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng