Mawaki Nura M. Inuwa ya samu karuwar da namiji
- Mawaki Nura M. Inuwa ya samu karuwar da namiji
- Tuni har an yi suna ya sakawa yaron suna Adam
- An dai daura auren jarumin ne a ranar Juma'a 28 ga watan Afrilu, 2017
Labarin da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa fitaccen mawakin nan na fina-finan Hausa mai suna Nura M. Inuwa ya samu karuwa a cikin satin da yagabata.
KU KARANTA: Yadda kaunar matata ta shiga zuciya ta - Mijin Alawiyya
Mun samu dai cewa jarumin ya samu da namiji wanda tuni har an yi suna ya sakawa yaron suna Adam kamar dai yadda muka samu.
Legit.ng ta tuna dai cewa jarumin yayi bukin kece raini ne kimanin watanni tara da suka shude a jihar Katsina inda aka shafe kwanaki ana shagulgula kafin daga bisani a daura auren a garin Malumfashi
Haka zalika mun samu dai cewa an daura auren jarumin ne a ranar Juma'a 28 ga watan Afrilu a garin na Malumfashi a wani kayataccen buki da ya samu halartar mutane da dama.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng