Dandalin Kannywood: Yadda kaunar matata ta shiga zuciya ta - Mijin Alawiyya ta Dadin Kowa
- Yadda kaunar matata ta shiga zuciya ta - Mijin Alawiyya ta Dadin Kowa
- Sharif Kamilu Inuwa ya bayyana yadda kauna da matukar soyayyar jarumar ta shiga zuciyar sa
- Fuskar jarumar na kama da ta mahaifiyar sa
A kwanan baya dai hakika auren da jarumar nan ta shirin wasan kwaikwayon nan na Dadin Kowa watau Khadija S. Islam watau Alawiyya ta yi shi ne ya dauki hankalin jama'a da dama musamman ma dai yadda jarumar take da matukar farin jini ga al'umma.
KU KARANTA: Kuruciya na damun Rahma Sadau - Ali Nuhu
To sai dai a wata fira da yayi da majiyar mu, wanda ya aure ta mai suna Sharif Kamilu Inuwa ya bayyana yadda kauna da matukar soyayyar jarumar ta shiga zuciyar sa lokaci daya.
Legit.ng dai ta samu cewa da yake bayar da ba'asi, Alhaji Kamalu ya bayyana cewa sun kai akalla shekaru hudu suna tare da jarumar kafin daga bisani ya aure ta a kwanan baya din.
Alhaji Kamalu ya bayyana cewa, yanayin matar ta sa na son addini, rashin wasa da sallah da kuma son wasa da kuma raha da jarumar ke da shi ne ya sanya yake matukar son ta.
Sannan kuma ya kara da cewa bayan haka kuma fuskar jarumar na kama da ta mahaifiyar sa wanda hakan ne ma yasa suka yi saurin shakuwa da ita.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng