Kungiyar kabilar Ibo na yunkurin haramtawa ‘yan uwansu cin naman Shanu
Rahotanni sun kawo cewa kungiyar matasan kabilar Ibo ta (Ohanaeze Nidgbo) ta yi kira ga gwamnonin yankinsu da su haramtawa al’umman yankin cin naman shanu kwata-kwata.
Shugaban kungiyar na kasa, Mazi Okechukwu Isiguzoro, wanda ya gabatar da kudirin a ranar Alhamis, ga watan Fabrairu, ya ce idan aka hana cin naman zai karfafa sha’anin tsaro a yankin, saboda a cewarsu sai ana cin naman shanu ne za a ga Fulani a wuri, idan ba a ci kuma shikenan.
Wannan furucin na kungiyar na da alaka da rikicin da ake samu tsakanin makiya da manoma a fadin kasar.
Matasan sun bukaci al’ummar yankinsu su nemi abin da za su maye naman shanun da shi, tun da wuri.
KU KARANTA KUMA: Ba a yi mani adalci ba kan rikicin makiyaya da manoma — Buhari
Sai dai kuma, a wani abu da za a bayyana da “an gudu ba a tsira ba” matasan sun ce mutanen yankin su rika kiwon shanun da za su ci namansu da kansu a garuruwa da kauyukansu.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Rundunar yan sandan Najeriya ta fara gudanar da bincike kan yadda jami'an rundunar ke gudanar da ayyukan su.
An bijiro da binciken ne domin gano ma'aikata cima zaune da kuma gurbatattun jami'ai cikin rundunar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng