Babu wani burin da muke dashi mu mamaye wani sashe na Najeriya
- Matsalar manoma da makiyaya ta zama ruwan dare inda kowanne bangare ke kashe dayan
- Abin ya gauraye da kabilanci da ma siyasa
- Shuggaba Buhari yace gwamnatinsu na iya kokarin magance lamarin
A ziyarar koke da shuwagabannin cocin katolica suka kai masa a jiya a fadar mulki, shugaba Buhari, ya sake jaddada musu cewa, kokarin sa na kawo zaman lafiya da sulhu tsakanin jama'un kasar nan, baya nufin mamaye wani yanki.
Su dai jihohin da abun ya shafa, na zargin shugaban ne da ko'in-kula da wahalwalu da ta'addancin makiyayan ke janyo musu.
Kokarin shugaban kuma na samar da wuraren kiwo ga Fulani a kowacce jiha, ya zama kamar mamaya ce wasu ke ganin ake shirin yi musu da wayau.
DUBA WANNAN: Adadin kudaden daa Najeriya ta samu a bara
Shi dai shugaba Buhari, ya taka sawun barawo ne, ganin cewa shi bafillace ne mai kiwon shanu, wasu na gani zayyi wuya yayi wa sauran kabilu adalci.
Har yanzu dai shugaban bai iya ziyartar koda jiha daya ba da makiyaya suka yi wa ta'addanci, sai dai ya gayyaci dattijansu zuwa wurinsa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng