Kididdigar kudaden da Najeriya ta samu a 2017 - inji CBN

Kididdigar kudaden da Najeriya ta samu a 2017 - inji CBN

- Farsashin man ffetur a duniya ya farfado daga komadar da yasha

- Ana tattala kudaden da aka samu ne daga albarkatun domin sama wa najeriya makoma

- An maida kudaden man Najeriya na wasoso a gwamnatocin baya

Kididdigar kudaden da Najeriya ta samu a 2017 - inji CBN
Kididdigar kudaden da Najeriya ta samu a 2017 - inji CBN

Babban bankin Najeriya CBN, ya fitar da kididdigar kudaden da Najeriya ta tara dag ffitar da danyen man fetur tun daga farkon shekarar bara zuwa karshenta. A shekarar ta 2017 ne dai aka fi samun dan hauhawar faarashin mai tun bayan da ya zube warwas a kasuwannin duniya.

A baran dai, Naira tiriliyan bakwai da biliyan 300 asusun Najeriyar ya samu. Kusan dai Naira tiriliyan 10 Najeriyar ta samu daga fitar da ababen musaya, kamar su kayan abinci, da kayan gona, wannan na nufin Najeriyar ta rage dogaro da man fetur a barar.

DUBA WANNAN: Sojin Najeriya sun yaba sun kuma gargadi 'yan agaji a yankin gabas

A cewar babban bankin, an sami ribar kusan tiriliyan uku, in aka kwatanta da ta bara biyu watau 2016, inda Najeriyar ta iya samun N5.8T kacal saboda ffaduwar arashin man na fetur a kasashen duniya, da ma daina sayen man na kasar nan da Amurka tayi tun a 2014, la'akari da hasashen hana fitar da man idan zabukan kasar suka zo da tangarda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng