Dandalin Kannywood: Kuruciya tare da daukaka ce ke damun Rahma Sadau - Ali Nuhu

Dandalin Kannywood: Kuruciya tare da daukaka ce ke damun Rahma Sadau - Ali Nuhu

- Kuruciya tare da daukaka ce ke damun Rahma Sadau - Ali Nuhu

- Ali Nuhu ya bayyana hakan ne a yayin da yake bayanin dalilin da yasa yake ta kokarin a maido da jarumar

- Yace zargin da ake yi masa na cewa ko yana so a maido da ita ne domin ya saka ta a cikin fim karya ne

Babban jarumin nan a masana'antar Kannywood watau Ali Nuhu ya bayyana jaruma Rahma Sadau a matsayin wadda kuruciya da kuma daukaka ke matukar damu inda kuma ya bukaci masu ruwa da tsaki a harkar fim din Hausa da suyi mata uzuri.

Dandalin Kannywood: Kuruciya tare da daukaka ce ke damun Rahma Sadau - Ali Nuhu
Dandalin Kannywood: Kuruciya tare da daukaka ce ke damun Rahma Sadau - Ali Nuhu

KU KARANTA: Na yafewa Momoh - Umma Shehu

Jarumi Ali Nuhu ya bayyana hakan ne a yayin da yake bayar da ba'asi game da muhimmin dalilin da yasa yake ta kokarin a maido da jarumar a masana'antar bayan korar ta da aka yi.

Legit.ng ta samu dai cewa Ali Nuhu ya kara da cewa, shi dai a iya sanin da yayi wa jarumar ba lallai bane ta kara aikata laifin da ta aikata don kuwa kullum ai dan adam na kara girma ne kuma hankali na kara shigar sa.

Haka zalika jarumin ya bayyana cewa zargin da ake yi masa na cewa ko yana so a maido da ita ne domin ya saka ta a cikin fim din sa kanzon kurege ne kawai babu kamshin gaskiya a ciki.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng