Dandalin Kannywood: Na yafe wa Aminu Momoh har lahira - Umma Shehu
- Na yafe wa Aminu Momoh har lahira - Umma Shehu
- Jarumar dai ta shiga takaddama a watannin baya bayan wata fira da ta yi a tashar Talabijin din Arewa 24
- Jarumar tace ita ta san ba da niyyar cin zarafin ta yayi
Jarumar nan ta wasan fim din Hausa da ta shiga takaddama a watannin baya bayan wata fira da ta yi a tashar Talabijin din Arewa 24 inda mai shirya shirin Aminu Momoh ya tambayeta wata tambaya game da addinin musulunci kuma ta ki amsawa watau Umma Shehu ta ce ta yafewa jarumin har abada.
KU KARANTA: Kiristoci sun fadawa Buhari matsalar da ake fuskanta
Umma Shehu tayi wannan kalamin ne a yayin da take fira da majiyar mu inda tace ita ta san ba da niyyar cin zarafin ta yayi mata wannan tambayar.
NAIj.com ta samu cewa jarumar ta bayyana cewa ita bata ga rashin kyautawar sa ba kuma ma ta san sana'ar sa yake yi domin gabadaya firar anyi ta ne cikin raha da dariya tun a watan Disembar shekarar 2016.
Haka nan kuma jarumar ta bayyana cewa ta ki ta ansa tambayar ne ba wai don bata san ansar ba a'a sai dai kawai don ta fuskanci shirin na nishadi ne da kuma harkokin fim ba wai na addini ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng