Cin-Hanci: Bada kudi ga alkali ba laifi bane, inji wani lauya

Cin-Hanci: Bada kudi ga alkali ba laifi bane, inji wani lauya

- An sha zargin alkalai da lauyoyida hada baki

- Ko a baya ma an kama wasu alkalai a Abuja da kudade a gidajensu

- Ana zargin lauyan da baiwa alkali toshiyar baki

Cin-Hanci: Bada kudi ga alkali ba laifi bane, inji wani lauya
Cin-Hanci: Bada kudi ga alkali ba laifi bane, inji wani lauya

A rananr Alhamis din nan ne, Dakta Joseph Nwobike (SAN), a babbar kotu dake Ikeja ya bayyana cewar babu laifi, idan mai laifi ko mai kara ya bawa alkali kudi, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar 2017. A lokacin da ake sharia akan cin hancin da ya karba.

Nwobike yana fuskantar sharia ne, saboda kama shi da aka yi da laifin cin hanci da rashawa, sannan kuma aka kama shi da laifin bawa hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), bayanan bogi.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa tace kimanin mutane miliyan bakwai ke amfana da tsarin samar da aikin yi

"Babu laifi a bawa alkali kudi, zai zama laifi ne kawai, idan lokacin da aka bashi kudin yana kan shari'a ne", inji shi.

Ko a baya ma dai, hukumar DSS ta zargi da kama wasu manyan alkalai na kasar nan, inda aka same su da kudade makil a gida, da ma a banki, da kuma karbar kudade daga wadanda ake tuhuma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng