Hukumar 'yan sanda ta nemi afuwa a wurin Kassim Afegbua saboda zargin shi data yi

Hukumar 'yan sanda ta nemi afuwa a wurin Kassim Afegbua saboda zargin shi data yi

- Hukumar 'yan sanda sun nemi afuwa a wurin Afegbua

- Sun nuna cewar kuskure ne yasa suka neme shi

- Afegbua ya kai karar hukumar 'yan sanda domin a bi mishi hakkin sa

Hukumar 'yan sanda ta nemi afuwa a wurin Kassim Afegbua saboda zargin shi data yi
Hukumar 'yan sanda ta nemi afuwa a wurin Kassim Afegbua saboda zargin shi data yi

A ranar Larabar nan ne Kassim Afegbua mai magana da yawun bakin tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ziyarci Hedkwatar 'Yan sanda dake Abuja, dangane da umarnin da Babban Sufeton 'Yan sanda, Ibrahim Idris ya bayar na kamo shi. Ya isa hedkwatar dake Louis Edet da misalin karfe 10.32 na safe tare da matarsa da kuma lauyan sa, Kayode Ajulo.

Da yake magana da manema labarai, kafin ya shiga hedkwatar, ya ce IBB, ya kira shi ya shaida mishi irin mamakin da yayi na kiran da 'yan sandan suka yi masa, inda ya kara da cewar takardar da ake son tuhumar sa akai ya rubuta tane da umarnin tsohon shugaban kasar.

DUBA WANNAN: Amurka: Ba za mu yaki Koriya ta Arewa ba

Afegbua ya kara da cewar, "A matsayina na dan Najeriya, ina ganin bai kamata ace an bada umarnin kamoni ba, ba tare da sanar dani ba, saboda haka na zo in gabatar da kaina." Ya bayyana cewar yayi karar hukumar 'yan sanda, da Channels TV da kuma NTA, domin a bi mishi hakkin shi na, saboda cin zarafin shi da suka yi. Sai dai ya kara da cewar ya umarci lauyan shi da ya janye karar akan Channels TV da NTA.

Da yake jawabi bayan ya gana da 'yan sandan, ya bayyana cewar yayi hira da Mataimakin Kwamishinan 'Yan sanda, sannan ya tabbatar mishi da cewar, sun janye duk wani zargi da suke akan shi. Sannan kuma sun nemi afuwa a gareshi, inda ya tabbatar mishi da cewar kuskure ne aka samu.

'Yan jarida sun tambayi lauyan shi akan ko zai janye karar da yake akan hukumar 'yan sanda, ya bayyana cewar ba zai iya cewa komai akai ba, dole sai sunje sun zauna sunyi shawara shi da mai gidan shi.

A ranar litinin din da ta gaba ta ne, hukumar yan sanda, ta bukaci a kamo Kassim Afegbua, saboda zargin shi da rubuta takarda ba tare da umarnin mai gidan shi ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.co

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng