Kotu tana tuhumar jami'in gwamnati da mallakar motoci 86

Kotu tana tuhumar jami'in gwamnati da mallakar motoci 86

- Kotun tarayya tana tuhumar wani da mallakar motoci 86

- Ana tuhumar shi da kannin sa domin gano gaskiyar motocin na waye

- Kotu ta bada belin su da umarnin su dawo wata mai zuwa

Ana tuhumar jami'in gwamnati da mallakar motoci 86
Ana tuhumar jami'in gwamnati da mallakar motoci 86

Wata babbar kotu a Najeriya, tana tuhumar wani babban jami'in gwamnati Ibrahim Tumsah, da kaninsa Tijjani, da kin tabbatar da wanda ya mallaki motocin alfarma 86 a cikinsu.

Ibrahim Tumsah, shi ne babban darakta mai kula da harkokin kudi a ma'aikatar ayyuka da gidaje ta kasa.

DUBA WANNAN: Wani dan sanda ya kashe dan acaba saboda ya hana shi cin hancin naira 100

Mutanen biyu, ana kuma zarginsu da kin bayyana kadarorinsu ba tare da wani kwararan dalilaiba.

Wani kwamiti na musamman da shugaba Muhammadu Buhari ya kafa don gudanar da bincike da kuma bankado kudaden gwamnati da aka sace ne ya bukaci Ibrahim Tumsah, da kaninsa a kan su bayyana ko motocin waye.

Yanzu haka dai an bayar da belinsu, tare da umartarsu a kan su sake bayyana gaban kotu domin ci gaba da shari'ar da ake musu a cikin wata mai kamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng