'Da naman mutane nake tsubbu wajen haɗa kuɗi'

'Da naman mutane nake tsubbu wajen haɗa kuɗi'

A ranar Alhamis din da ta gabata ne, hukumar 'yan sanda ta jihar Oyo, ta cafke wasu mutane hudu da laifin cin karensu ba bu babbaka wajen kasuwancin sassan jikin dan Adam a yankin Ayegun na birnin Ibadan.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Abiodun Odude ya bayyana cewa, daya daga wannan miyagun mutane, Sulaiman Hamed dan shekaru 35 da ya shahara da sunan Alfa, ya saba jagorantar sallolin gawa, inda bayan an binne wani mamaci sai ya aika wasu mutane biyu domin yanko masa sassan jiki na gawar da zai gudanar da tsubbace-tsubbacen sa na neman duniya.

Miyagun kenan bayan sun shiga hannu
Miyagun kenan bayan sun shiga hannu

Wannan mutane biyu; Olapade Saheed da kuma Olatunji Abiodun, sun shiga hannu ne a yayin da jami'ai suka cafke su da sassan jiki na wata gawa, da hakan yayi sanadiyar taso keyar Alfa da kuma wani abokin huldarsa da yace shi fasto ne a cocin Ojagbo ta unguwar Oranyan.

KARANTA KUMA: Ma'aikatan jihar Kano sunyi barazanar yajin aikin akan rage musu albashi

Alfa ya bayyana cewa, ya kan biya N2, 500 ga duk wanda ya kawo masa sassan jikin dan Adam da yake amfani da su wajen tsubbace-tsubbacen sa na neman duniya.

Kwamishinan 'yan sandan ya kara da cewa, hukumar za ta kare zage dantsen ta domin taso keyar 'yan ta'adda a jihar.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, gobarar dare tayi mummunan ta'adi a wata kasuwar wayoyin salula ta jihar Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng