Mulkin Najeriya ba na wasu tsirarun mutane ba ne, dole mu hada karfi da karfe wuri guda – Saraki
- Shugaban majalisar dattijai, Abubakar Bukola Saraki, ya ce mulkin Najeriya ban a bangaren zartarwa ba ne kadai
- Ya bukaci bangarorin gwamnati su hada karfi da karfe domin kawo karshen tashe-tashen hankula da suke neman zama ruwa dare a Najeriya
- Saraki na wannan kalamai ne a yau, Ahamis, yayin bude taro na musamman da majalisar dattijai ta shirya domin tattauna batun tsaro
A yau ne majalisar dattijai ta fara gudanar da wani taro na musamman domin tattauna yadda za a shawo kan yawaitar tashe-tashen hankula da suke nema su zama tamkar ruwan dare a kasar nan.
Tun a watan da ya gabata ne majalisar ta so gudanar da taron amma dole ta daga shi saboda bangaren zartarwa sun nuna shakku a kan manufar taron kamar yadda Legit.ng ta wallafa labarai a kai.
Da yake jawabi yayin bude taron, Saraki, yace akwai bukatar hadin kai tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa domin kawo karshen matsalolin tsaro da kusan duk sassan kasar nan ke fama da su.
“Makasudin kafa gwamnati shine kare jama’a da dukiyoyinsu. Batun tsaro ba na mutum daya ba ne, abu ne dake bukatar hadin kan dukkan bangarorin gwamnati da jama’a ma bakidaya. Buhari kadai da bangaren zartarwa ba zasu iya ba, akwai bukatar mu hada karfi da karfe domin kawo karshen matsalolin satar mutane, rikicin makiyaya, fashi da makami, garkuwa da mutane, da dukkan matsalolin tsaro dake damun Najeriya,” a cewar Saraki.
DUBA WANNAN: Zidane ya yanke shawarar yin bankwana da kungiyar Real Madrid
Saraki ya ci gaba da cewa “dukkannin mu nan masu ruwa da tsaki ne a harkar mulkin Najeriya, muna da gudunmawar da zamu iya bayar wa domin tabbatar da zaman lafiya a Najeriya.”
Saraki ya nuna damuwar sa bisa yadda rayuka ke salwanta a kullum sakamakon rikicin kabilanci da aiyukan ‘yan ta’adda tare da yin kira a hada kai, ba tare da la’akari da banbancin siyasa ba, domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng