Dokar hana kiwo a Benue: Kotu ta kama saurayi da laifin kiwon shanu
- Rikicin makiyaya a jihar Benue ya kai ya kawo
- An maida kiwo babban laifi a jihar
- An kama saurayi da laifin kiwo a gonakin mutane
Tun bayan hawansa kan karagar mulki, gwamnan jihar Binue ta tsakiyar Najeriya, ya hana kiwo a jiharsa, inda ya sanya dokar kame duk wani bafillace da yake kiwo.
Su dai fulanin sun maida martani, inda sukan farma kauyuka da kashe-kashe da sare-sare, da ma kone kone, musamman idan an saci shanunsu.
Bidiyo da ake da yadawa a soshiyal midiya na nuna irin barnar da bangarorin suka yi wa juna, musamman na kwanakin nan, inda akan ga makiyaya da bindigogi a cikin gonakin mutane suna cin doya.
An kuma kama samari da yawa da gwamnatin jihar ta baiwa makamai domin rangadi da aikin kula da kame makiyaya da suka bi daji.
DUBA WANNAN: An koma gidan jiya, Shekau yayo sabon bidiyo
A yau dai alhamis, wata kotu ta sami wani saurrayi da irin wannan laiffin na kiwo, inda wasu mata uku suka kaishi kara da cewa ya kai shanunsa kiwo cikn gonakinsu.
Shi dai sauratin, ya amsa laifinsa, inda bai musa ba cewa yayi kiwon dabbobin a harabar gonakinsu, amma kuma ga alama bai ma san hakan ya haramta a jihar ba.
Jihar daai, ta hana kiwo na shanu wanda fulani kan yi musamman a lokutan da ruwan arewa ya janye.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng