Dandalin Kannywood: Kun ji abun da aka yi wa tsohuwar jaruma Muhibbat Abdussalam

Dandalin Kannywood: Kun ji abun da aka yi wa tsohuwar jaruma Muhibbat Abdussalam

- Kun ji abun da aka yi wa tsohuwar jaruma Muhibbat Abdussalam

- Sure Start Initiative ta zabi tsohuwar jarumar wasan Hausa ta masana'antar Kannywood sannan ta kuma karramata

- A wajen bukin karramawar an rabawa matan da suka halarta kayan tsaftar jiki da na kula da yara

Wata kungiyar sa kai da ba ta gwamnati ba mai rajin yaki da kanana da ma manyan cututtukan dake addabar mata mai suna Sure Start Initiative ta zabi tsohuwar jarumar wasan Hausa ta masana'antar Kannywood sannan ta kuma karramata da lambar yabo.

Dandalin Kannywood: Kun ji abun da aka yi wa tsohuwar jaruma Muhibbat Abdussalam
Dandalin Kannywood: Kun ji abun da aka yi wa tsohuwar jaruma Muhibbat Abdussalam

KU KARANTA: Mansura Isa ta yi abun kirki a Kaduna

Kungiyar dai ta bayyana cewa ta karrama jarumar ne bisa la'akari da ta yi da irin gudummuwar da take bai wa cigaban kungiyar wajen yakar cututtukan da kan addabi mata a al'ummar mu ta hanyar shirin da take gudanarwa a gidan Talabiji.

Legit.ng dai haka zalika ta samu cewa a wajen bukin karramawar an rabawa matan da suka halarta kayan tsaftar jiki da na kula da yara da ma wasu kayayyakin masarufi wanda yana daya daga ckin manufofin assassa kungiyar daman.

Ita ma da take tsokaci, Muhibbat din ta bayyana matukar jin dadin ta game da karramawar da aka yi mata sannan kuma ta bukaci dukkan al'umma da su cigaba da baiwa kungiyar cikakken goyon baya.

Fitattun jaruman fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood da dama da suka hada da Aminu Momoh da Halima Atete sun kwashi 'yan kallo a yayin bukin bayar da kyaututtuka na City People Awards da aka saba yi duk shekara.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng