Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa nike so a yafewa Rahma Sadau - Ali Nuhu

Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa nike so a yafewa Rahma Sadau - Ali Nuhu

- Dalilin da yasa nike so a yafewa Rahma Sadau - Ali Nuhu

- Yace jarumar ta hanyar sa ce ta shiga masana'antar kuma ta amince da da ta aikala laifin

- An gan shi tare da jarumar sun fito daga ofishin shugaban hukumar tace fina-finan

Babban jogo sannan kuma daya daga cikin manyan jarumai, masu bada umurni, koya rawa kuma jigo a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood watau Ali Nuhu ya bayyana dalilin da yasa ya dage lallai lallai sai an dawo da Rahma Sadau harkar fim bayan korar ta da akayi.

Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa nike so a yafewa Rahma Sadau - Ali Nuhu
Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa nike so a yafewa Rahma Sadau - Ali Nuhu

KU KARANTA: Ali Nuhu da Adam A. Zango duk azzalumai ne - Ali Artwork

Ali Nuhu din dai ya bayyana cewa ganin cewa jarumar ta hanyar sa ce ta shiga masana'antar kuma ta amince da da ta aikala laifin sannan kuma har ta nemi afuwa da gafara daga wajen duk masu ruwa da tsaki, shi ne ma dalilin da yake ganin ya kamata a yafe wa jarumar hakanan.

Legit.ng ta samu cewa ya yi wannan bayanin ne ga wakilin majiyar mu jim kadan bayan an gan shi tare da jarumar sun fito daga ofishin shugaban hukumar tace fina-finan Hausa Watau Alhaji Afakallahu in da ake kyautata zaton ya jagorance ta ne ta je ta bashi hakuri.

Sai dai da aka tambaye shi ko yana so ya shirya wani fim ne da kuma yake da muradin saka jarumar, sai ya kada baki yace shi fim din sa da yake aiki a kan sa yanzu shine 'Abota' kuma tuni an gama tsara labari babu jaruma Rahma Sadau a ciki.

A wani labarin kuma, Wani marubuci mai suna Yakubu M. Kumo ya caccaki BMB kan zagi da yayiwa shahararren jarumin nan na kamfanin shirya fina-finan Hausa Ali Nuhu. An zargi darakta kuma mai shirya wasa Bello Muhammad Bello da cewa mahaifin Ali Nuhu Kirista ne.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng