Dandalin Kannywood: Ganduje ya dauki nauyin horas da 'yan fim 450
- Ganduje ya dauki nauyin horas da 'yan fim 450
- Hukumar dake sa'ido ga harkokin fina-finai tare kuma da tace su ta jihar Kano zata kula da hakan
- shirin da suka bullo da shi zai horar da mutane 150 ne sau uku a kowane zango
Hukumar dake sa'ido ga harkokin fina-finai tare kuma da tace su ta jihar Kano a karkashin jagorancin Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ta sanar da niyyar ta ta horas da yan fim akalla 450 a wani yunkuri na ganin ta kara tsaftace harkar ta fina-finai a jihar.
KU KARANTA: Ina matukar son Aure - Sadiya Kabala
Shugaban hukumar dake sa'ido ga harkokin fina-finai tare kuma da tace su ta jihar Kano watau Alhaji Isma'ila Na'abba wanda aka fi sani da Afakallah shine ya sanar da hakan a yayin kaddamar da fara gudanar da shirin a jihar ta Kano.
Legit.ng ta samu dai cewa da yake bayani, ya bayyana cewa a matsayin su na shugabanni sun lura akwai karancin kwarewa a harkar ta fina-finan shiyasa ma suka hada gwuiwa da babbar hukumar dake horas da sana'ar ta kasa domin koyar da yan jihar.
A cewar sa, shirin da suka bullo da shi zai horar da mutane 150 ne sau uku a kowane zango kuma za' tabo kowane bangare na masu shirya fim di.
A wani labarin kuma, Fitattun jaruman fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood da dama da suka hada da Aminu Momoh da Halima Atete sun kwashi 'yan kallo a yayin bukin bayar da kyaututtuka na City People Awards da aka saba yi duk shekara.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng