Dandalin Kannywood: Mansura Isah ta yi wani abun kirki a jihar Kaduna

Dandalin Kannywood: Mansura Isah ta yi wani abun kirki a jihar Kaduna

- Mansura Isah ta yi wani abun kirki a jihar Kaduna

- Mansura Isa ta yi wa wasu masu karamin karfi sha-tara-ta-arziki a garin Kaduna.

- Ta raba kayan abincin ne ga mabukata da dama a karkashin Gidauniyar Today's Life Foundation

Tsohuwar jarumar wasan Hausa ta masana'antar Kannywood kuma uwar gidan fitaccen jarumin nan na fagen wasan Hausa watau Sani Danja mai suna Mansura Isa ta yi wa wasu masu karamin karfi sha-tara-ta-arziki a garin Kaduna.

Dandalin Kannywood: Mansura Isah ta yi wani abun kirki a jihar Kaduna
Dandalin Kannywood: Mansura Isah ta yi wani abun kirki a jihar Kaduna

KU KARANTA: Momo da Atete sun kwashi yan kallo a Legas

Mun samu dai cewa tsohuwar jarumar ta raba kayan abincin ne ga mabukata da dama a karkashin inuwar kungiyar ta mai suna Gidauniyar tallafawa rayuwa watau Today's Life Foundation kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu.

Legit.ng ta samu dai cewa tsohuwar jarumar ta samu rakiyar wata tsohuwar jarumar takwarar ta watau Fati KK da Wasila Isma'il wadanda dukkanin su sun yi fice a zamanin su da ma wasu kawayen su mata da dama.

Kayayyakin da Hajiya Mansura ta raba dai sun hada da Shinkafa, Biredi, garin tuwo, indomie , ome, sabulu da ma dai dukkan sauran kayan masarufi.

A wani labarin kuma, Fitattun jaruman fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood da dama da suka hada da Aminu Momoh da Halima Atete sun kwashi 'yan kallo a yayin bukin bayar da kyaututtuka na City People Awards da aka saba yi duk shekara.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng