Dandalin Kannywood: Aminu Momoh da Halima Atete sun kwashi 'yan kallo a birnin Legas

Dandalin Kannywood: Aminu Momoh da Halima Atete sun kwashi 'yan kallo a birnin Legas

- Aminu Momoh da Halima Atete sun kwashi 'yan kallo a birnin Legas

- Sun kwashi 'yan kallon ne a yayin bukin bayar da kyaututtuka na City People Awards

- Aminu Sherif Momoh ne ya lashe kyautar gwarzon jarumin yayin da ita kuma Halima Atete ce ta lashe rukunin jarumai

Fitattun jaruman fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood da dama da suka hada da Aminu Momoh da Halima Atete sun kwashi 'yan kallo a yayin bukin bayar da kyaututtuka na City People Awards da aka saba yi duk shekara.

Dandalin Kannywood: Aminu Momoh da Halima Atete sun kwashi 'yan kallo a birnin Legas
Dandalin Kannywood: Aminu Momoh da Halima Atete sun kwashi 'yan kallo a birnin Legas

KU KARANTA: Buhari ya amince a gina sabbin hanyoyin jirgin kasa

Mun samu dai cewa Mujallar ta City News da ke zama a birnin Legas ce ke shirya wannan bikin duk shekara inda kuma takan karrama masu ruwa da tsaki a harkar fim na Najeriya kama daga Furodusoshi zuwa jarumai da daraktoci da dai sauran su.

Legit.ng dai ta samu cewa a bukin mujallar na shekarar 2017, Jamrumi Aminu Sherif Momoh ne ya lashe kyautar gwarzon jarumin yayin da ita kuma Halima Atete ce ta lashe rukunin jarumai na mata.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a watannin baya masana'atar ta Kannywood ta shiga cece-kuce bayan da Jarumi AMinu Momoh ya so ya kunyata jaruma Umma Shehu a yayin wani shiri da yake gabatarwa a gidan Talabijin na Arewa 24.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng