Kungiyar WFP ta ciyar da ‘yan Najeriya miliyan daya a shekara 2017

Kungiyar WFP ta ciyar da ‘yan Najeriya miliyan daya a shekara 2017

- Kungiyar WFP ta yi ikrarin ciyar da 'yan Najeriya miliyan daya a shekara 2017

- A karshen shekara 2017 'yan Boko-haram suka kai wa tawagar kungiyar Majalissar Dinkin Duniya hari da sace kayan abincin da suka dauko

Kungiyar dake taimakon mutane da abinci na duniya (WFP) ta tallafawa ‘yan Najeriya miliyan daya kayan abinci a yankin Arewa maso gabas a shekara 2017.

Wakilin kungiyar WFP, Myrta Kaulard ya bayyana haka a ne a hirar da yayi da manema labarun News Agency of Nigeria (NAN) a ranar Alhamis.

Kungiyar WFP ta ciyar da ‘yan Najeriya miliyan daya a shekara 2017
Kungiyar WFP ta ciyar da ‘yan Najeriya miliyan daya a shekara 2017

Kungiyar WFP tana karkashin kungiyar majalissar Dinkin Duniya, kuma ita ce babban kungiyar da ke tallafawa mutane da abinci.

KU KARANTA : INEC zata watsa sakamakon zaben 2019 ta hanyar tauraron dan Adam

“Mun tallafawa mutanen miliyan daya a yankin Arewa masu gabashin Najeriya da kayan abinci saboda sun rasa gidajen su da dukiyoyin su ta sanadiyar rikicin kungiyar Bok-haram.

A karshen shekarar da ta gabata Legit.ng ta rawaito labarrin yadda mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari kan tawagar motocin jami’an Majalisar Dinkin Duniya a Jihar Borno inda suka kashe mutum hudu, suka kuma gudu da kayan abinci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng