Shugaban kungiyar Boko Haram ya baiwa mayakansa sabon umarni

Shugaban kungiyar Boko Haram ya baiwa mayakansa sabon umarni

Shugaban kungiyar ta’addanci na Boko Haram, Abubakar Shekau ya baiwa mayakan Boko Haram sabon umarni ta yadda zasu tafiyar da yake yaken da suke yi, ba kamar yadda suke yi a baya ba.

Rariya ta ruwaito Shekau ya bayyana haka ne cikin wani sabon bidiyo da ya fitar, inda ya umarci mayakansa akan su fara yi ma abokan yakinsu nasiha, idan kuma suka ki bin nasihar, toh su hallakasu.

KU KARANTA: An yanke ma matar da ta caka ma Mijinta wuka, hukuncin kisa ta hanyar rataya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shi yana fadin: “Duk inda kuka ga mai akidar bin dokokin nijeriya, ku yi masa nasiha, idan kuma bai ji ba ku bindige shi.” Inji Abubakar Shekau.

Shugaban kungiyar Boko Haram ya baiwa mayakansa sabon umarni
Shekau

A wani labarin kuma, Shekau ya koka kan yadda kungiyarsu ke fuskantar bala’I tare da kuntatawa daga rundunar Sojojin Najeriya, inda yace da wannan bala’in da yake fuskanta, gara ya mutu ko ya shiga aljanna ya huta.

“Na gaji da wannan fitinar, gara ma in mutu, na tafi na huta a Aljanna.” Inji shugaban yan ta’adda na kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng