Wannan masifar ta ishe ni, na gaji - Abubakar Shekau

Wannan masifar ta ishe ni, na gaji - Abubakar Shekau

Shugaban kungiyar jama’atu ahlus sunnanli da’awati wal jihad wanda akafi sani da Boko Haram ya saki wani sabon faifan bidiyo ind aya bayyana cewa shi fa ya gaji da wannan masifa, ya kosa ya mutu kawai ya shiga Aljannah.

A cikin sakon bidiyon na harshen hausa kuma na minti 10, Shekau ya bayyana matukar takaicinsa kan yadda ake kashe ‘yan kungiyarsa kuma ya ce, hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

A cikin Faifan bidiyon mai tsawon minti 10, shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ya bayyana bakin cikinsa game da yadda jami’an soji ke ragargazan mayakansa.

Game da cewar masu sharhi, babu wani alamar zafi da karsashi ya saba nunawa wanann karon. Ga dukkan alama ya gaji da yakin kamar yadda muryarsa ta nuna.

Kwanaki hudu da ikirarin hukumar soji na samun nasara a kan kungiyar ta Boko Haram, sai ga shi a yau shugaban kungiyar, Abubakar Shekau, ya bayyana a wani sabon faifan bidiyo yana karyata maganar rundunar soji tare da daukan alkawarin kai wasu sabbin hare-hare.

Wani masifar ta ishe ni, na gaji - Abubakar Shekau
Wani masifar ta ishe ni, na gaji - Abubakar Shekau

Da yake tabbatar da sahihancin faifan bidiyon, mutumin da ya saka faifan bidiyon a shafinsa na Tuwita, Ahmad Salkida (Dan jarida), ya bayyana cewar a bayyane take cewar Shekau da mayakan kungiyar Boko Haram ba wuri daya suke zaune ba.

KU KARANTA: Hukumar DSS ta sammaci mai magana da yawun IBB, Kassim Afegbua

Wasu rahotonni dai sun bayyana cewar Shekau ya tsere daga maboyar sa tare da wasu mutane, ciki har da matan 'yan sanda, da yake rike da su sa'o'i kadan kafin dakarun sojin su dirar wa maboyar sa a dajin Sambisa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng