Kuma dai: Hukumar DSS ta sammaci mai magana da yawun IBB, Kassim Afegbua
Hukumar tsaron leken asiri ta sammaci Kassim Afegbua, mai magana da yawun tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida, Kassim Afegbua.
Mr Kassim ya samu wannan gayyata ne ta wayar salula inda hukumar ta bukaci ya halarta a ofishinta kafin karfe 11 na safiya yau tare da lauyansa, Kayode Ajulo.
An gayyacesa ne bayan ya mika kansa ga hukumar yan sanda a shelkwatanta da ke Abuja sakamakon sammacin da suka masa na cewa yayi rubutun da ka iya tayar da hankalin jama’a a madadin tsohon shugaban kasa, Ibrahim badamasi Babangida.
Zaku tuna cewa jaridar Legit.ng ta kawo muku rahoton jawabin da tsohon shugaba IBBya saki ranan Lahadi inda ya bukaci shugaba Buhari kada ya sake takara a 2019.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng